Assault

Kebbi: Sojoji Sun Ceto Mutane 11 Da Aka Sace

FANSA 1
FANSA 1

Sojojin rundunar haɗin gwiwa dake aiki a yankin  Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a wasu samame daban-daban da aka gudanar a garin Ribah da yankin Wasagu-Falfala na Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu a Jihar Kebbi.

 

Cikin sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, a ranar 30 ga watan Oktoba 2026, sojojin dake aiki a sashi na 2 sun amsa wani  kiran gaggawa kan wasu ‘yan ta’adda da suka tare hanyar Ribah zuwa Dirindaji yayin da suke ƙoƙarin kutsawa garin Ribah, bayan isarsu wurin, ‘yan ta’addan sun tsere da mutane bakwai, lamarin da ya sa sojojin suka bi sawunsu zuwa ƙauyen Rambo, inda matsin lambar sojojin ya tilasta musu sakin mutanen.

 

Sanarwar ta ce wadanda aka ceto su hada da  Sa’adu Bala, mai shekaru 53, Nura Musa, 25, Dantami Yahyi, 57, Nasiru Muhammad, 21, Abdulhakeem Abubakar, 23, Abdulahi Maikudi, 32, da Zaki Gambo, 56. dukkansu ‘yan asalin Ribah ne kuma an sada   su da danginsu.

 

A wani samame kuma, a ranar 31 ga Oktoba 2026, sojojin  da ke sintiri a yankin Wasagu-Falfala domin kare al’umma da hana ‘yan ta’adda gudanar da ayyukansu, sun fada tarkon kwanton bauna da aka yi musu. Sai dai sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fatattaki ‘yan ta’addan da ƙarfin wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa . Yayin da sojojin ke binciken yankin bayan artabun, sun gano wasu mutane huɗu da ‘yan ta’addan suka bari a wurin.

 

Wadanda aka ceto su ne: Lawali Ali, mai shekaru 20; Samaila Shaibu, 14; Kasimu Shaibu, 20; da Aliyu Bala, 18. Dukkansu mazauna ƙauyen Wasagu ne, kuma an miƙa su ga dagacin ƙauyen domin sake haɗa su da iyalansu.

Rundunar ta ce sojojin na ci gaba da gudanar da sintiri da mamaye yankin domin ƙara tabbatar da tsaro da kuma hana ‘yan ta’adda sake kai hare-hare.

 

Operation FANSAN YAMMA ta jaddada cewa za ta ci gaba da kare rayukan al’umma masu bin doka da oda  da ke ƙarƙashin kulawarta, ta kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da baiwa  jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan tsaro da kuma dakile hare-haren ‘yan ta’adda.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *