Assault

Kano: ‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Sace Dagaci a Gezawa

FB IMG 1793468501886
FB IMG 1793468501886

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta dakile wani yunkurin satar dagacin kauyen Bangare da ke karamar hukumar Gezawa, tare da kama wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a shirin.

Crime Detail ta rawaito cewa wannan na cikin sanarwar da rundunar ‘yan sandan Kano ta fitar, inda tace lamarin ya faru ne bayan Mallam Idris, Wanda shine dagacin kauyen Bangare, ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Gezawa da misalin karfe 1:30 na dare a ranar 26 ga Oktoba, 2026, cewa a ranar 24 ga Oktoba da misalin karfe 9:33 na dare, cewa wani mutum da bai san ko wanene ba ya kira shi ta waya yana yi masa barazanar cewa za a sace shi.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda na Gezawa suka fara bin diddigin lamarin ta hanyar amfani da bayanan sirri da binciken kwararru.

Hakan ya kai ga cafke Aliyu Naziru Garba, mai shekaru 20, da Bashir Alhasan, mai shekaru 20, wadanda rundunar ta ce sun amsa laifin su.

A halin yanzu ana ci gaba da bincike, kuma bayan kammala binciken, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar tuhume-tuhumen hada baki wajen aikata laifi, yin barazana da kuma yunkurin satar mutum.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an dake aiki a Gezawa bisa daukar matakin gaggawa da kwarewa wajen dakile shirin.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci duk Wani yunkurin ta’addanci ba, yana mai cewa nasarar ta yi daidai da tsarin aikin babban Sufeton ’yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu wanda ya mayar da hankali kan amfani da bayanan sirri, fasahar zamani, kwarewa da kuma daukar matakan kariya tun kafin aikata laifi.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *