Assault

Sojoji Sun Kama Mutumin Da Ake zargi Da Yin Garkuwa Yayin Da Yake Kokarin Karbar Kudin Fansa

whirlstroke
whirlstroke

Rundunar Haɗin Gwiwa, Operation WHIRL STROKE, tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar DSS, sun kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da mutane a wani samame na sirri da aka shirya bisa sahihin bayanan sirri. An kama wanda ake zargin ne yayin da yake shirin karɓar kuɗin fansa  Naira 200,000, wanda ake zargin ya nema daga wata mata da ya yi  barazanar yin garkuwa da ita.

Lamarin ya faru ne a ranar 29 ga Oktoba 2026, bayan jami’an DSS sun sanar da sojoji cewa wata mace  na fuskantar barazana daga wani mutum mai suna Mukaila Iliyasu.

Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya buƙaci matar ta biya shi ₦200,000, tare da yi mata barazanar sace ta idan ba ta cika masa wannan buƙata ba. Bayan samun rahoton, sojojin da jami’an DSS sun haɗa kai wajen shirya samamen kama wanda ake zargin.

Wani soja ne dai yayi basaji, inda ya kai kuɗin da ake nema ga wanda ake zargin, sannan aka cafke shi a daidai lokacin da yake karɓar kuɗin.

Bayan kama shi, an miƙa wanda ake zargin ga jami’an DSS domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

Kwamandan Operation WHIRL STROKE kuma babban Kwamandan runduna ta 5 ta sojojin Najeriya, Manjo Janar Moses Kolo Gara, ya yabawa sojojin da jami’an DSS bisa nuna ƙwarewa, jarumtaka da haɗin gwiwa, tare da umartar su da su ci gaba da inganta musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar aiki domin dakile garkuwa da mutane da sauran barazanar tsaro a yankin da ke ƙarƙashin ayyukansu.

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *